Monday, 11 June 2018

Shugaba Buhari yayi ganawa da Sarki Muhammad VI na kasar Morocco: Sun sakawa yarjejeniyar kasuwanci hannu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ganawa da sarkin Morocco,Muhammad VI inda wakilan kasashen biyu suka saka hannu akan yarjejeniyar kasuwanci data hada da ajiye bututun iskar Gas daga Najeriya zuwa kasar ta Morocco.Ajiye bututun Gas din daga Najeriya wanda zai bi ta kasashen yammacin Afrika zai kai zuwa kasar ta Morocco kuma ya wuce zuwa wasu kasashen turai.

A wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar ya fitar, Malam Garba shehu ya bayyana cewa, kasashen biyu sun kuma saka hannu akan horas da manoman Najeriya akan hanyoyin adana amfanin gona.
kuma wakilan kasashen biyu sun saka hannu akan bude ma'aikatar sarrafa ma'adanin Ammonia a Najeriya wanda dashine ake yin takin zamani da sauran abubuwan amfani

No comments:

Post a Comment