Friday, 29 June 2018

Shugaba Buhari zai halarci taron kungiyar kasashen Afrika da za'ayi a kasar Mauritania

Gobe, Asabar idan Allah ya kaimu, shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai tafi kasar Mauritania inda zai halarci taron kungiyar kasashen Afrika wanda shuwagabannin Afika daban-daban zasu halarta.


Bayan taron shugaba Buhari zai gana da shuwagabannin kasashe dan tattauna dangantakarsu da Najeriya haka kuma shugaba Buhari zai shiga wata ganawa da za'ayi da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron akan tsaro a Nahiyar Afrika, kamar yanda sanarwar me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesin ya fitar ta bayyana.

A cikin wanda zasu wa shugaba Buhari rakiya akwai gwamnan Nasarawa, Tanko Almakura dana Edo, Godwin Obaseki da sauran manyan jami'an gwamnati.

No comments:

Post a Comment