Tuesday, 12 June 2018

Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya tafi da bayinshi na tafi da gidanka kasar Singapore dan kada makiya su saci kashinshi

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya je kasar Singapore inda suka tattauna da shugaban kasar Amurka da bayinshi na tafi da gidanka, saboda tsoron kada makiya su dauki samfurin kashinshi su san halin da lafiyarshi take ciki.


Wani tsohon dogarine da ya taba yin aiki a kasar ta koriya ta Arewa amma daga baya ya tsere zuwa koriya ta kudu ya shaidawa Washington post da wannan labari. Dogarin ya kara da cewa duk inda Kim zashi baya amfani da bandakin da sauran jama'a ke amfani dashi, yana da nashi na tafi da gidanka wanda ake ware mota daya daga cikin motocin da zasu mai rakiya a ajiyeshi a ciki,dabarar itace dan kada makiya su dauki samfarin kashinshi su san halin da lafiyarshi ke ciki.

Zuwan Kim kasar Singapore da jirage biyu yaje, jirgi na farko ya fara sauka wanda ke dauke da kayan abincinshi da motarshi ta musamman da bandakinshi na tafi da gidanka, dayan jirgin kuma shine a ciki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun daga tashin shi zuwa kasar ta Singapore aka fara shirya dabaru dan kada makiya su harbo jirginshi, an shirya jirage uku dan yin basaja saboda kada a gane wannene yake ciki, kuma jiragen sun rika tashi da tazarar awa daya tsakanin juna.

Haka kuma Kim ya canja hanyar daya kamata ace itace yabi da zata kaishi kasar Singapore kai tsaye, inda sai da yayi zagaye wanda hakan ya tsawaita tafiyar tashi da awanni goma.

Wannan dai itace tafiya mafi nisa da yayi daga kasar tashi tun bayan da ya amshi ragamar mulkin kasar, sannan itace ta uku, ta farko yaje China ta biyu yaje koriya ta Kudu sannan sai wannan da yazo Singapore.
Haka kuma bayan saukarshi a filin jirgin saman kasar Singapore anga dogarannan nashi masu zagaye motarshi dan bata kariya idan tana tafiya zagaye da shi suna sassarfa. A karin farko da aka ga wadannan dogarannashi lokacin da ya kai ziyara kasar Koriya ta kudune wanda hoton ya dauki hankulan mutane sosai.

No comments:

Post a Comment