Tuesday, 12 June 2018

Shugabannin Yarbawa Na Ci gaba Da Jinjinawa Buhari Kan Baiwa Abiola Lambar GfCR

Shugabannin Yarbawa na ci gaba jinjinawa Shugaba Muhammad Buhari bisa matakin da ya dauka na baiwa Marigayi M.K.O Abiola Babbar lambar girmamawa ta kasa wato, GFCR a yau a ranar 12 ga watan Yuni wadda rana ce da aka soke zaben Shugaban kasa da marigayin ya lashe a 1993.


Tuni dai, Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa wannan mataki da Buhari ya dauka na girmama Abiola ya sa dole ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Buhari yakin neman zabe a shekarar 2019 inda ya nuna yin haka girmamawa ce ga daukacin Yarbawa.

Shi kuwa dan fitaccen lauyan nan Marigayi Gani Fawehenme wanda shi ma ya samu lambar girmamawa duk da yake a lokacin yana raye ya ki karbar lambar, Mohammed Fawehenme ya nuna cewa babu wani Shugaba a tarihin Nijeriya da ya san abin da ya dace irin Shubaga Buhari.

Haka nan kuma Shugaba Buhari ya amince da baiwa wasu Fitattun 'yan siyasa da suka taka rawa a dimokradiyyar Nijeriya lambar girmamawa. Da yake tabbatar da haka Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa ya ce nan bada jimawa za a fitar da sunayen wadannan 'yan siyasar.
rariya

No comments:

Post a Comment