Wednesday, 13 June 2018

Sifaniya ta bayyana Farnando Heirro a matsayin sabon kocin kasar bayan korar Jolen Lopegui

Biyo bayan korar kocinta, Jolen Lopetegui daga aikin horas da kungiyar kwallon kafarta,kasar Sifaniya ta bayyana Farnando Heirro a matsayin wanda zai cigaba da horas da 'yan kwallon a gasar cin kofin Duniyar da za'a buga a kasar Rasha.


Masu sharhi na ganin cewa wannan korar me horas da 'yan wasan ana kwana biyu da fara gasar cin kofin Duniyar zai iya shafar yanayin buga wasan 'yan kwallon, shidai Farnando tsohon me wasan bayane na kungiyar Bolton Wanderes sannan kuma shine daracta na kungiyar kwallon kafar kasar ta sifaniya.

No comments:

Post a Comment