Wednesday, 13 June 2018

Spain ta kori kocinta Jolen Lopetegui saboda amsar aikin horas da Real Madrid ba tare da sanar da itaba

Spain ta kori kocinta Julen Lopetegui bayan sanar da cewar shi ne sabon kocin Real Madrid.
Spain ta kore shi duka kwana biyu kafin wasanta na farko a gasar cin kofin duniya inda za sa kara da kasar Portugal a ranar 15 ga watan Yuni.


A ranar Talata Real Madrid ta bayar da sanarwar cewar Lopetegui ne kocin da zai gaji Zinedine Zidane a Bernabeu.

Hukumar kwallon kafa ta Spain ta ce ta kori Lopetegui mai shekara 51 saboda ya kulla yarjejeniya da Real Madrid ba tare da sanar da ita ba.

Za fara gasar cin kofin duniya ne ranar Alhamis a Rasha.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment