Saturday, 9 June 2018

Taron G7: An ware Trump kan ciniki da Rasha

Bambance-bambance kan Rasha da cinikayya sun fito fili tsakanin Shugaba Trump da sauran shugabannin kungiyar G7 a Kyanada.


Shugaban na Amurka ya ba sauran shugabannin mamaki a lokacin da yayi kira da a kyale Rasha ta dawo cikin kungiyar, bayan da aka kore ta saboda kwace yankin Crimea da tayi.

Amma shugabar Jamus Angela Merkel ta ce dukkan shugabanni daga Tarayyar Turai (EU) da ke halartar taron kolin sun yi watsi da batun.

Akwai kuma batun shingayen ciniki da karin haraji da Shugaba Trump ya saka wa kawayen cinikin Amurka da ke neman rusa dukkan wani yunkuri na sasantawa a wajen taron.

Kasar Kyanada ta kira sabbin jerin harajin "haramtattu", inda shi kuma shugaban majalisar Turai Donald Tusk ya gargadi Mista Trump cewa matakan da ya dauka za su kasance babban hatsari.

Amma bayan tattaunawa da Mista Trump, Shugaba Emanuel Macron na Faransa ya ce "abubuwa na kan hanya" kuma da akwai sauran dama ta samun cigaba. Amma bai bayar da karin bayani ba.
BBCHausa.

No comments:

Post a Comment