Thursday, 28 June 2018

Wadanda Aka Sayarwa Kamfanonin Wutar Lantarki 'Yan Damfara Ne>>Majalisa

Majalisar Wakilai ta koka yadda kamfanonin raba wutar lantarki ke cutar masu hulda da su inda majalisar ta nuna cewa mafi yawan wadanda aka sayarwa kamfanonin sun kware wajen iya damfarar jama'a.


Shugaban kwamitin wanda ya binciki yadda kamfanonin ke cutar 'yan Nijeriya ta hanyar tsawwala masu kudin wutar lantarki na majalisar , Hon. Israel Ajibola Famurewa ya ce, kamfanonin sun samu daurin gindin ne daga hukumar kula da kamfanonin wutar lantarki ta kasa wadda hakkinta ne ta sanya masu ido tare da Ladaftar da su.
rariya

No comments:

Post a Comment