Thursday, 28 June 2018

Wai me yasa idan Namiji da mace suka je siyayya sai a rika tambayar namijin kudin kayan da suka siya?>>Nafisa Abdullahi

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta bayyana wani abu dake ci mata tuwo a kwarya, abin kuwa shine irin yanda idan mace da namiji suka je gurin siyayya sai a rika tambayar na mijin kudin kayan da suka siya.


Nafisar ta bayar da misalin zuwa siyayya da tayi tare da wani ma'aikacinta, tace, bayan sun kammala daukar abubuwan da zasu siya sai me shagon ya baiwa ma'aikacin nata takardar biyan kudi, tace, sai ta jira ma'aikacin nata ya miko mata takardar.

Bayan ya miko mata sai ta cewa me shagon to nice zan biya, Nafisa tace, me shagon yayi ta bata hakuri yace yana fatan bata ji haushi ba, ta gayamai cewa, taji kuma ya sani su mata suna iya ma kansu siyayya dama abinda yafi haka.

Ta kara da cewa idan taje kasar waje suka je siyayya da mutane ana tambayar sune mutum daya ne zai biya kudin kayan ko kuwa hadaka zasuyi?.

1 comment:

  1. Wannan ya taso ne domin mu a al'adar mu ta Hausa, na miji ke biya ma mace kaya ko wani abubuwan saye a mapi yawan lokutta, saboda haka bai ma kamata ba ta ji wani haushi don ba a bata takardar biya ba. A can kasar waje kuwa, kamar a China ko kuma wata kasar ta daban ai su suna hada gwia ne domin biyan abubuwan da suke saya, kamar cewa na miji bai dauki nauyin komai a kansa ba. Mi sali idan kana da abokiya mace kuka je sayan kayyayyaki , za ku iya hada kudi ku sauya, domin bai zama dole namijin ya saya mata ba! Saboda haka, al'ada ce ta ka hakan da kuma Muslinci, " Arijalu qawwamuna alannisa'i" fadar Alqur'ani kenan cewa "Maza suna da fifici a kan mata" saboda nauyin dawainiya da Allah ya dora a kan su na matan da iyalin su.

    ReplyDelete