Saturday, 9 June 2018

Wani Musulmi ya kashe kanshi a Ka'aba

Wani mutum da ba a tantance ba ya fado daga saman kololuwar Masallacin Ka'aba a Makkah a daidai lokacin da mutane ke dawafi.


Kamfanin dillacin labaran Saudiya SPA ya ambato 'yan sandan kasar na cewa nan take mutumin ya mutu bayan fadowarsa.

Sai dai ba a bayyana abin da ya yi dalilin fadowarsa ba daga kololuwar saman masallacin na Haram a Makkah ba.

"An tafi da gawarsa zuwa asibiti, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano asalinsa da kuma abin da ya haddasa fadowarsa daga sama duk da an kewaye saman da waya" kamar yadda SPA ya ruwaito.

Kamfanin dillacin labaran Saudiyar kuma ya ce ana tunanin mutumin ya kashe kansa ne domin ba wannan ne karon farko ba da hakan ta faru a Masallacin na Ka'aba, yayin da Addinin Islama ya haramta kisan kai.

Al'amarin ya faru yayin da musulmi ke azumin Ramadan, a lokacin da kuma dubban al'ummar musulmi ke gudanar da Ibadah a Masallacin mai tsarki a Makkah.

A bara wani ya yi kokarin cinna wa kansa wuta a gaban Ka'aba, kafin jami'an tsaro suka hana shi.
BBCHausa.

No comments:

Post a Comment