Tuesday, 12 June 2018

Wani sabon bincike ya kunno kai da ake tuhumar Bukola Saraki da barnatar da wasu makudan kudade

Bukola Saraki ya sake shiga sarkakiya a hannun 'yansanda, kan wasu biliyoyi
Mista Bukola Saraki, Sanata yanzu kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, zai zama bako ga bangare na musamman na binciken damfara, karkashin hukumar yan sandan Najeriya a Legas, inda suke da bukatar ya ansa tambayoyi dangane da lalata Naira biliyan 11 a tsohon bankin Intercontinental Plc. 

Majiya mai karfi tace Mista Lekan Alabi, tsohon shugaban bankin Intercontinental yana tsare saboda wannan binciken. 

Masu bincike suna kokarin gano yanda manyan basussuka na sama da Naira biliyan 11 suka samu hanyar shiga kamfanin saida man fetur, Joy Petroleum, mallakin daya daga cikin mataimakan Saraki, amma yanzu ya mutu. 

Masu binciken, kamar yanda majiyar mu tace, suna so Saraki ya taimaka musu gurin gane yanda akayi amfani da kadarorin shi na kasuwar Ikoyi da Victoria Island a Legas gurin karbar basussukan da ba a biya ba amma an goge su kuma an bar kadarorin da akayi amfani aka karbi bashin. 

"Zan iya fada muku cewa, ana tuhumar Mista Alabi ne saboda wannan dalilin," cewar majiyar mu wanda ya yarda cewa nan kusa za'a gayyaci gwamnan jihar Kwara na yanzu, Mista Abdulfatai Ahmed, tunda da yawan kudin an karbe su ne a lokacin da yake kwamishinan kudi a karkashin Gwamnatin Saraki.

No comments:

Post a Comment