Sunday, 10 June 2018

Wani yaro ya roki Suarez dan Allah kada yayi cizo a gasar cin kofin Duniya

Wani yaro masoyin tauraron kwallo, Suarez ya rokeshi da cewa dan Allah ya daure wannan karin kada ya ciji kowa a gasar cin kofin zakarun turai da za'a buga a kasar Rasha, yaron ya gayawa Suarez hakanne a lokacin da Suarez din yake saka hannu a rigar yaron.


Suarez dai ya gantsarawa Georgio Chiellini cizo a gasar cin kofin da aka buga a kasar Brazil wanda hakan yasa aka bashi jan kati da kuma haramta mishi buga wasanni tara, wancan din dai ba shine karin farko da Suarez ke yin cizo ana tsaka da kwallo ba.

No comments:

Post a Comment