Wednesday, 20 June 2018

Wannan kyakkyawar baiwar Allahn na tuna shekaru 7 da suka gabata lokacin da ta zama gurguwa

Wannan kyakyawar baiwar Allahn da rashin lafiya ya sameta wanda yayi dalilin komawarta gurguwa, yanzu take amfani da keke guragu, ta tuna da shekaru bakwai da suka gabata, lokacin da ibtila'in ya sameta.Tace a duk shekara idan ta tuna da wannan rana takan ji bakin ciki amma wannan karin abin zai zama na daban, ita dai wannan baiwar Allah na matukar burge mutane musamman a shafukan sada zumunta saboda karfin gwiwar ta da kuma kyan da Allah ya mata.Muna mata fatan Alheri da kuma Allah yasa wannan abu ya zamar mata kaffarar zunubanta.

No comments:

Post a Comment