Thursday, 14 June 2018

Wasanmu da Najeriya ba mai sauki bane - Messi

media
Gwarzon dan wasan Argentina Lionel Messi, ya ce duk da cewa tawagar kwallon kasarsa, ba ta da cikakkiyar masaniya kan kwarewar ‘yan wasan Najeriya, tabbas ya san wasan da zasu fata a gasar cin kofin duniya a bana ba mai sauki bane.


Argentina da Najeriya da ke rukuni na hudu tare da kasashen Crotia da Iceland, zasu fafata ne a filin wasa da ke Saint Petersburg ranar 26 ga watan Yuni da muke ciki.
Har yanzu dai Najeriya na kan kokarin ganin ta samu nasarar lallasa Argentina, a manyan wasannin da suke haduwa, la’akari da cewa a wasanni 4 Najeriya ta yi da Argentina a shekarun 1994, 2002, 2010 da kuma 2014, 'yan wasan Najeriyar basu taba samun nasara kan takwarorinsu na Argentina ba, idan aka dauke wasan sada zumuncin da suka taba lallasa su da kwallaye 4-1.
rfihausa.

No comments:

Post a Comment