Saturday, 9 June 2018

Watakila Ronaldo ya fasa barin Madrid: An mai karin albashi kuma am rufe tuhumar rashin biyan harajin da ake mishi

Wasu sabbin rahotanni sun bayyana cewa, bayan tattaunawa ta tsawon lokaci tsakanin wakilin Cristiano Ronaldo da kungiyar Real Madrid, kungiyar ta yarda ta karamai albashi zuwa miliyan ashirin da biyar a shekara.


AS ta ruwaito cewa wani dan jarida me suna Manolo Lama da akayi hira dashi a wani gidan rediyo ya bayyana cewa Real Madrid din ta karawa Ronaldo Albashi inda yanzu zai rika daukar miliyan talatin da biyu da dubu dari biyar a shekara.

Kudin dai sun kunshi ainihin albashinshi wanda aka karamai ya zama miliyin ashirin da biyar a shekara sai kuma miliyan bakwai da dubu dari biyar wanda suka kunshi wasu ihisani da aka mishi saboda, daukar kofin Laliga, Copa del Rey, cinye kyautar tauraron dan kwallon FIFA, cinye kyautar gwarzon dan kwallon Ballon D'or da kuma bayyana da yake yi a fili.

Ronaldo dai na neman karin albashi daga miliyan ashirin da daya da ake biyanshi zuwa miliyan talatin da bakwai a shekara, abinda ke ciwa Ronaldo tuwo a kwarya shine irin yanda takwarorinshi, Neymar da Messi ke daukar kusan miliyan arba'ain duk shekara kowannen su a kungiyoyin da suke wa wasa amma shi gashi nan yana daukar rabin abinda suke dauka.

Ronaldo na ganin cewa matsayinshi yafi karfin albashin da Real Madrid ke biyanshi.

Dan jaridar yace da Ronaldon zai yi hakuri zai iya samun sauran kudin da yake nema ta hanyar tallace-tallacen da zai rika yiwa kamfanoni. 

Da aka tambayi dan jaridar ko me zice akan labarin daya bayyana cewa Ronaldon ya riga ya cire rai da sake bugawa Real Madrid wasa, bayan da sukace ba zasu karamai albashiba, yana ganin wannan karin da aka mishi zaisa ya canja ra'ayinshi?.

Sai yace gaskiya abin akwai sarkakkiya da yawa a ciki, amma watakila Ronaldon ya canja ra'ayi.

A wani labarin kuma rahotanni sun tabbatar da cewa an rufe zargin da akewa Ronaldon na kin biyan haraji wanda a da akace zai iya sawa yayi zaman gidan kaso, yanzu Ronaldon ya yarda da laifin nashi kuma zai biya wancan kudin harajin da ake binshi da suka kai Yuro miliyan sha tara, hakan yasa aka rufe maganar tuhumar da ake mishi.

No comments:

Post a Comment