Thursday, 28 June 2018

Yadda liman ya boye Kiristoci a masallaci a rikicin Filato


Lokacin da wani limamin masallaci ya ga mutane sun shigo kauyensa da ke jihar Filato ranar Lahadi, bai yi wata-wata ba ya bude kofarsa ya karbe su.

Mutanen da suka gudo kauyen nasa sun fito ne daga wani kauye mai makwabtaka da karamar hukumar Barikin Ladi, inda wasu da ake tunanin makiyaya ne suka shiga kuma suka yi kashe-kashe tare da lalata abubuwa.

Kimanin mutum 262 limamin ya bai wa mafaka, inda ya shigar da mata cikin gidansa, maza kuma saka maza a masallaci.

'Yan sanda sun ce mutum 86 suka mutu a hare-haren, amma mutanen kauyen sun ce wadanda suka mutu sun haura 200.

Limanin ya shaida wa wakiliyar BBC cewar: "Na fara shigar da mata a cikin gidana domin boye su, sannan mazansu kuma na ba su mafaka a cikin masallaci."

Da yawa daga cikin 'yan kabilar Berom sun tsere ne tare da wasu Musulman dake zaune a kauyen nasu zuwa kauyen dake kusa.

'Yan bindigar sun samu limamin suna neman kiristocin da ya boye domin su kashe su, amma bai yarda ba.

Ya yi karyar cewar dukkan mutanen da ke cikin masallacin Musulmai ne. Ya roki 'yan bindigar kuma suka amince suka tafi.

Ta hanyar limamin ne dai kiristocin 'yan kabilar Berom da ke kauyen suka tsira daga harin.

A yanzu haka dai sun rasa muhallinsu, suna zama ne a cikin masallacin.

A shekarun baya al'ummar Musulman garin sun kasance suna neman filin da za su gina masallaci, kuma 'yan kabilar Berom ne suka ba su filin a kyauta domin su gina masallacin.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment