Tuesday, 12 June 2018

Yadda ya kamata Najeriya ta tunkari Rasha 2018>>Garba Lawal

Yayin da ake tunkarar gasar cin kofin duniya da za a fara a kasar Rasha nan da kwana uku, tsohon dan wasan tawagar Super Eagles, Garba Lawal, ya yi tsokaci game da yadda ya kamata 'yan wasan Najeriyar na yanzu su tunkari gasar.


A wata hirar da ya yi da BBC, Lawal, wanda yake cikin wadanda suka wakilci Najeriya a gasar a shekarar 1998, ya nuna cewa kada 'yan wasa su damu da tsoron jin ciwo in suna son taka rawar gani.

Lawal ya ce dabarar wasa a hankali a cikin fili ba zai taimaki dan wasa ba wajen kauce wa rauni domin tsautsayi na iya zuwa ko ta wace hanya.

Tsohon dan wasan Roda JC na kasar Holland din ya ce duk wanda ya je gasar na son ya ci gasar.

Sai dai kuma dan wasan ya ce ko wane dan wasa ya san lokacin da ya kamata ya huta bayan ya dawo daga atisaye domin samun isasshiyar lafiya da hutun da jikinsa ke bukata.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment