Saturday, 23 June 2018

'Yan Najeriya sun fi son Ahmad Musa fiye da Shugaba Buhari: Anyi kira Musan ya fito takarara shugaban kasa

Bayan kayatattun kwallayen da Ahmad Musa yaci a wasan da Najeriya ta buga da kasar Iceland a lokacin da Najeriyar ke neman nasara wurjanjan dan kada a dawo da ita gida daga gasar cin kofin Duniya, wasu 'yan Najeriyar sun bayyana cewa sunfi son Ahmad Musa din da shugaba Buhari kuma suna kira a gareshi da ya fito takarar shugaban cin kasarnan.


Wani shafin yanar gizo yayi kuri'a akan wa 'yan Najeriyar suka fi so tsakanin Ahmad Musa da Shugaba Buharin? Shugaba Buhari ya samu kuri'u sama da dubu biyu shi kuwa Ahmad Musa ya samu kuri'u sama da dubu takwas.
'Yan Najeriya da dama sun rika yin hotunan fastar neman shugabancin kasa ga Ahmad Musa din suna sakawa a shafukan sada zumunta.

No comments:

Post a Comment