Thursday, 28 June 2018

'Yan Najeriya sun yi farin ciki da fitar da Jamus daga gasar cin kofin Duniya

Bayan fitar da Najeriya daga gasar cin kofin Duniya da kasar Argentina tayi, mutane da dama sunyi bakincikin hakan inda wasu suka rika fitowa shafukan sada zumunta suna bayyana bacin ransu.


A jiyane aka cire Jamus, kasar dake rike da kofin Duniyar a yanzu, wannan cirewa da akawa Jamus ya sa da dama daga cikin 'yan Najeriya da suka damu lokacin da aka cire Super Eagles sun dan ji dama dama.

Wasu ma sun nuna farin cikinsu a fili inda suka rika fadin ga wanda suka zo da kofin ma gaba daya kuma kwararrune a harkar kwallo an fitar dasu, to namu da sauki-sauki, da dama sun rika farin ciki da wannan labari a shafukansu na sada zumunta.

No comments:

Post a Comment