Sunday, 10 June 2018

‘Yan sanda sun kara gano wata alaka mai karfi tsakanin ‘yan fashin Offa da Saraki

A cigaba da binciken da take gudanarwa a kan ‘yan fashin da suka tafka barnar rayuka da dukiyoyin al’umma a garin Offa, jihar Kwara, hukumar ‘yan sanda ta kara gano cewar, 5 daga cikin shugabannin ‘yan fashin sun halarci bikin diyar Bukola Saraki, shugaban majalisar dattijai.


'Yan fashin sun amsa cewar tabbas sun halarci bikin diyar Bukola da aka yi wasu watanni kafin fashin garin Offa.

A wani jawabi da hukumar ‘yan sanda ta fitar, ta bayyana cewar 3 daga cikin ‘yan fashin na daga cikin mutanen da suka raka Saraki ziyarar jaje da ta’aziyya ga mutanen garin Offa bayan fashin na ranar 5 ga watan Afrilu.

Tuni hukumar ‘yan sanda ta bukaci ya bayyana a gaban ta domin wanke kan sa daga zargin hannun sa cikin fashin garin Offa kafin daga bisani ta janye gayyatar tare da bukatar shi ya rubuto hujjojin kare kan sa zuwa ga hukumar cikin sa’o’i 48.

Bukola Saraki ya musanta cewar yana da hannu a cikin fashin duk da har yanzu bai musanta batun cewar ‘yan fashin na yi masa aiki ba.

No comments:

Post a Comment