Monday, 11 June 2018

'Yar kabilar Igbo, Musulma, A'ishat Obi ta musuluntar da 'yan uwanta 5

Inyamurar nan data karbi addinin musulunci a kwanakin baya ta kuma dage da yin da'awa inda take janyo 'yan uwanta inyamurai shiga addinin musulunci, ta kuma bayyana wasu 'yan uwanta Inyamurai data musuluntar a jihar Rivers.


Ga abinda Malama Aishat Obi  ta rubuta a shafi ta na facebook:

"Allahu Akbar, Asalamu alaikum 'yan uwana musulmai maza da mata. Ku taya ni murnar shigowar wasu 'yan yankunan kudu maso kudu da kudu maso gabashin kasar nan cikin addinin musulunci a jiya a garin Fatakwal.

Sunayen su sune kamar haka:

(1) Believe Isaiah (Sehid Isaiah)  (daga jihar Rivers)

(2) Okechukwu Onwusaraka (Isan Onwusaraka) (daga jihar Imo)

(3) Chinonso Onyejiako (Hassan Onyejiako) (daga jihar Imo)

(4) Ngozi Uwa (Nafisa Hassan) (daga jihar Imo) 

(5) Oluchi Eze (Khadija Eze) (daga jihar Imo)

Malama Aishat Obi ta kuma yi fatan Allah ya kare ta tare da ba ta nasara a da'awar da take yi don ganin ta jawo 'yan uwanta Inyamurai cikin addinin Musulunci.

No comments:

Post a Comment