Friday, 29 June 2018

Zamu dawwama a talauci muddin bamu rage haihuwa barkatai ba>>Ministan Buhari

Ministan Kasuwanci da saka jari, Mr. Okechukwu Enelamah ya ce Najeriya za ta cigaba da dawwama cikin talauci muddin yan Najeriya basu dena haihuwan yara barkatai ba.


Ministan ya furta wannan magana ne a ranar Laraba yayin da ya ke tsokaci a kan rahoton Brookings da ta bayyana cewa Najeriya ce kasa mafi yawan al'umma da ke fama da talauci a Duniya.

"Ina tunanin ya kamata mu zage damtse a muyi aiki tukuru a matsayinmu na 'yan Najeriya, idan ba muyi hakan, mutanen mu za su cigaba da haihuwan yara barkatai kuma suna kara dilmiyewa cikin talauci," inji shi.

"Ya kuma yi korafi a kan rahoton kasashen duniya mafi talauci da aka fitar cikin kwanakin nan inda ya ce cibiyar binciken da dauka alkallumanta ne lokacin da Najeriya ke cikin halin matsin tattalin arziki.

No comments:

Post a Comment