Saturday, 23 June 2018

Zuwan Bukola Saraki Rasha ne ya baiwa 'yan Super Eagles sa'ar da suka samu akan Iceland

Kakakin majalisar dattijai da wasu sanatoci sun gana da Ahmad Musa a kasar Rasha bayan rawar ganin daya taka a nasarar da Super Eagles suka samu jiya akan Icelanda a gasar cin kofin Duniya.


Shugaban marasa rinjaye a majalisar, Godswill Akpabio da shukagaban hukumar kwallo, NFF ta Najeriya, Amaju Pinnick sun gana da Ahmad Musa din sun kuma jinjinamai da kara mai karfin gwiwa.

Ahmad Musa ne dai yaci duka kwallaye biyun na Super Eagles kuma shine gwarzon dan kwallo a wasan.

Amaju Pinnik ya bayyana cewa, zuwan kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki gurin 'yan wasan ya kawo musu sa'ar nasarar da suka samu akan Iceland din, ya kuma godewa wakilan da shugaba Buhari ya aika kasar Rashar bisa karfin gwiwar da suka kara ma 'yan wasan.

Wasa na gaba dai tsakanin Super Eagles ne da Argentina.

No comments:

Post a Comment