Sunday, 1 July 2018

2019: Jam’iyyun adawa sun hada-kai za su yi wa APC taron dangi dan kayar da Buhari

Mun samu labari daga Jaridar Tribune cewa manyan Jam’iyyun adawan kasar nan sun gama shirye-shiryen yadda za su tika Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kasa a zabe mai zuwa na 2019.


Kusan dai ba shakka Jam’iyyar APC za ta tsaida Shugaba Buhari ne a matsayin ‘Dan takarar Shugaban kasa a zaben na 2019 don haka ne Jam’iyyun adawar Kasar kusan 40 sun hada-kai za su yi wa Shugaba Buhari taron dangi.

Labarin da mu ke samu shi ne Jam’iyyar adawa ta PDP da Takwarar ta SDP da LP a ADC da kuma wasu ‘Yan nPDP na daf da sa hannu a wata yarjejeniya inda su ka zari takobin fatattakan Shugaba Buhari daga kujerar Shugaban kasa.

Majiyar ta mu ta bayyana cewa manyan Jam’iyyun sun yi wani taro inda su ka cin ma matsaya cewa dole a yaki Shugaba Buhari a 2019 saboda yadda Najeriya ta samu rabuwar kai da kuma matsaloli ta fannoni da dama a Gwamnatin nan.

Yanzu dai abin da ya rage shi ne a fitar da Jam’iyyar da za ayi amfani da ita a 2019. Kuma a mako mai zuwa ne za ayi wani babban taro a Garin Benuwe inda manyan Kudancin kasar nan da ‘Yan siyasar Arewa ta tsakiya za su sa labule game da 2019.

No comments:

Post a Comment