Monday, 2 July 2018

A karo na shida: Kotu ta bayar da belin Sambo Dasuki

Alleged Fund Diversion: FG Files Amended Charges Against Dasuki
Babban kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin tsohon me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Sambo Dasuki, wannan ne dai karo na shida da kotu ke bayar da belin shi amma hukummar 'yan sandan farin kaya ta DSS taki sakinshi.Kotun ta bayar da belin na Dasuki akan kudi naira miliyan dari biyu da kuma mutane biyu da zasu tsayamai, kowane daga cikin mutane biyun zai bayar da naira miliyan dari kuma kowane dale ya kasance yana matsayi na 16 a aikin gwamnati idan kuma ba ma'aikacin gwamnati bane dole ya kasance yana da gida ko gini a yankin Asokoro, Utako, Garki, Maitama dake babban birnin tarayya Abuja.

Alkaliya Ijeoma Ojukwu ta bayyana tsare Dasuki da akayi na tsawon shekaru biyu da rabi a matsayin abinda ya sabawa doka, sannan ta bayyanawa hukumar DSS cewa basu da hurumin hukunta mutum, kotu ce kawai ke da wannan hurumin, dan haka nan gaba idan zasu yiwa Dasukin tambaya ba sai sun kamashi ba kuma dole ya zamana ranar aikice.

Dasuki ya bukaci kotun data umarci gwamnati ta biyashi biliyan biyar na batamai lokaci da suna da akayi amma kotun tace tunda ta bayar da beli yanzu ba zata iya biyan wannan bukata tashi ba.

Gwamnatin tarayya na tuhumar Dasuki ne da karkatar da kudin makamai sama da dala biliyan biyu
Channels.

No comments:

Post a Comment