Monday, 9 July 2018

Abin dariyane ace akwai hannun mu ni da Saraki a fashin Offa>>Inji gwamnan Kwara Abdulfatah

A wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ya bayyana cewa dangantasu da fashin bankin da akayi a garin Offa na jihar abin dariyane.


Yace, abin dariyane ace, yanda suke kokari da kuma yin amfani da duk abinda suke dashi wajan inganta rayuwar jama'a da kuma samar da tsaro na tsawon shekaru wai kuma ace suna da hannu a shirin lalata wannan tsari.

Rahotanni dai sun bayyana cewa wasu daga cikin 'yan fashin da aka kama suna sata a bankin sun bayyana cewa su yaran kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki ne da gwamna Ahmad amma sun kara da cewa ba sune suka aikasu yin wancan fashi ba.

No comments:

Post a Comment