Thursday, 19 July 2018

Abin kunya da ban mamaki: Karanta yanda aka zambaci kungiyar kwallo ta Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar Ingila ta fada cikin wani yanayi na damfara da zamba cikin aminci da wani mutum dan kasar China ya mata, abinda ya baiwa mutane da dama mamaki sannan kuma ya zama abin kunya ga ita Arsenal din.


A watan Afrilun wannan shekara da muke ciki Arsenal ta bayyana hadin gwiwa da wani kamfanin kasar China me suna BYD Auto amma daga baya ta bayyana cewa wannan abu yaudarace domin kuwa wanda ya sakawa takardar alkawarin hannu ba ma ma'aikacin kamfanin BYD Auto din bane.

Da dama abin ya daure musu kai ta yanda akayi kungiyar kwallo kamar Arsenal ta samu kanta a cikin wannan cakwakiya.

A sakon data fitar a wancan lokaci, Arsenal ta bayyana cewa suna alfahari da kuma farin cikin kasancewa kungiyar kwallon kafa ta Ingila ta farko da tayi hadin gwiwa da kamfanin yin motoci masu amfani da wutar lantarki na Duniya, wanda babban kamfanine a kasar China, sun kara da cewa motoci masu amfani da lantarkine nan gaba zasu mamaye Duniya, suna farin cikin yiwa daya daga cikin kamfanin dake kan gaba a wannan harka maraba da hada hannu dasu.

Saidai wani rahoto da Daily Mail ta wallafa ya bayyana cewa mutumin da Arsenal tayi wannan yarjejeniya dashi bama ma'aikacin kamfanin bane, an bayyana sunanshi da Li Juan  kuma yanzu haka 'yan sanda sun kamashi ana bincikenshi a birnin Shanghai.

Haka kuma kamfanin ya fitar da sanarwa inda yace hankalinshi yakai kan wani rahoton karya da aka wallafa na cewa zaiyi huddar kasuwanci da wasu wanda wani mutum me suna Li Juan yayi amfani da shaidar boge ta kamfanin da kuma tambarin boge wajan sakawa waccan yarjeje niya hannu.

Yanzu haka dai Li Juan yana hannun hukuma.

A takardar alkawarin za'a rika tallata kamfanin BYD a filin wasan Emirates da buga sunanshi a jikin kujerun zama  filin kwallon.

No comments:

Post a Comment