Thursday, 19 July 2018

Abinda Ngolo Kante yayi a wannan hoton ya dauki hankulan mutane

Wannan hoton da tawagar 'yan kwallon kafar kasar Faransa suka dauka da shugaban kasarsu, Emmanuel Macron rike da kofin Duniya da suka lashe daga kasar Rasha ya dauki hankulan mutane saboda mutane sun rika tambayar wai ina Ngolo Kante ne?.


Kante dai gajeren mutum ne, rahotanni sun bayyan cewa; yafi ko wane dan kwallo a gasar cin kofin Duniya ta 2018 da aka kammala a Rasha kai farmakin kwace kwallo.

A lokacin da wannan hoton na sama ya fara yawo a shafukan sada zumunta, mutane sun rika tambayar wai ina Kante ya shige ne?, amma daga baya da aka duba hoton da kyau an hangoshi can a bayan Griezmann.

Kante ba irin mutanen nanne masu son nuna kansu ba, koda a lokacin da 'yan kwallon Faransar keta kokarin rike kofin Duniyar suna daukar hoto dashi a Rasha, shi be damu da yin hakan ba, saida wasu daga cikin abokan aikin nashi suka lura sannan suka ce ya kamata a bashi shima ya dauki hoto da kofin.

Wani abu dake kara nuna saukin kai da kuma soyayyar dake tsakanin Kante da abokan aikinshi shine, bayan sun dauki kofin Duniya sun koma dakin canja kaya 'yan kwallon Faransar sun rika rerawa Kante wakar yabo.

No comments:

Post a Comment