Sunday, 1 July 2018

Ahmed Musa na murnar cika shekara daya da yin aure

Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmad Musa na murnar cika shekara daya da yin aure, Musa ya fitar da wani sako a dandalinshi na sada zumunta inda yace, yana taya matar tashi murnar wannan rana.Yace tabbas Rahama ce samunta a rayuwarshi, yace na godewa Allah da ya kawoki cikin rayuwata kuma ina rokon Allah ya albarkacemu da karin shekaru. Ina sonki.

No comments:

Post a Comment