Tuesday, 10 July 2018

Allah ya rigada ya kadarta cewa Buhari zai fadi a zaben 2019>>Galadima

Alhaji Buba Galadima, shugaban kungiyar sabuwar APC (R-APC) ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ajiye kudirinsa na sake takara a 2019 saboda zai sha kashi.


Galadima, wadda kungiyarsa ta R-APC ta hade da sauran jam’iyyun siyasa a ranar Litinin, 9 ga watan Yuli, yace Allah ya kaddata cewa shugaba Buhari zai fadi a zaben 2019.

Ya kuma yi zargin cewa mambobin kungiyar siyasar sa na fuskantar barzanar mutuwa tunda suka bar APC ta hanyar sakonni.

Ya kara da cewa sun kuma samu sakonnin yarjejeniya tunda suka balle daga jam’iyya mai mulki.

Galadima, wadda a kwanan nan ya bayyana cewa ya kasance tare da Buhari tun a 2002 sannan kuma shine sakataren jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC), ya bayyana cewa shugaban kasar ya san cewa ba lallai ne yayi nasarar zabe ba.

No comments:

Post a Comment