Thursday, 12 July 2018

An gano wani Kabari mai rikitarwa a Masar

A yayin wani haka da ake na neman kayan tarihi a garin Iskandariyya da ke arewacin Masar an samu wani Kabari mai rikitarwa.


Kwararrun da ke aikin ba su bude Kabarin ba har yanzu.

Labaran da mujallar Science Alert ta fitar na cewa,  kwararrun sun bayyana kabarin a matsayin mafi girma da aka samu a Iskandariyya.

Kabarin na da tsayin santimita 185, fadin santimita 165 da kuma tsayin santimita 265 kuma an binne shi a kasa a shekarun 305 zuwa 30 kafin Miladiyya a zamanin mulkin Masarautar Ptoleme.

Yadda murfinsa ya ke a manne na nuna cewa, sama da shekaru dubu 2 ba a taba bude shi ba.

Makabartu kadan ne suke a Masar ba tare da barayi sun je sun lalata wasu kayan da ke cikinsu ba.

An samu wani dutse fari da ke kusa da Kabarin wanda ake kyautata zaton na mutumin da aka binne ne.

Masnaan Kimiyya sun ce, alamu sun nuna Kabarin na wani Babban Mutum ne Mai Matsayi.
trthausa.

No comments:

Post a Comment