Wednesday, 11 July 2018

An gargadi 'yan sanda su rage kiba ko su rasa aikinsu

Wata rundunar 'yan sanda a Indiya ta gargadi jami'anta da su rage teba ko kuma a sallame su daga aiki.


Shugaban 'yan sanda na Karnataka State Reserve Police ya shaida wa BBC cewa ya damu da yadda matsalar kiba ke karuwa a cikin yawancin jami'an rundunar.

Bhaskar Rao ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan da fiye da 'yan sanda 100 suka mutu a cikin wata 18 da suka gabata saboda matsalar kiba.

Amma ya ce za a taimaka ma 'yan sandan wajen da hanyoyin da za su kula da lafiyarsu.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Karnataka na da jami'ai fiye da 14,000, kuma akan neme su da su kwantar da tarzoma, da kuma tabbatar da tsaro a fadin jihar.

Yawancin jami'an da ke fama da matsalar kiba na cin abinci kamar shinkafa da soyayyen abinci. An gano cewa su na shan taba, kana ba sa motsa jiki.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment