Friday, 13 July 2018

An hana Musulmai yin Sallar Juma'a a Tajmahal

An hana Musulmai yin Sallar Juma'a a Tajmahal da ke garin Agra na Indiya wanda daya daga cikin wuraren ban mamaki na duniya ne.


Jaridar Indian Times ta rawaito cewa, Kotun Kolin Indiya ce ta zartar da hukuncin na cewa, Tajmahal na daya daga cikin wurare 7 na duniya masu ban mamaki a saboda haka dole ne a tsare shi.

Kotun ta ce, akwai masallatan Juma'a da dama a Agra. Masu son yin Slalah su je can su yi..

Hukuncin ya kuma bayyana cewa, dukkan masu son yin Sallah a Masallacin da ke Tajmahal dole su nuna shaidar cewa,suna rayuwa a garin Agra.

A shekarar 1631 ne Shah Jihan ya gina Tajmahal karkashin Daular Hint-Turk.
trthausa.

No comments:

Post a Comment