Monday, 9 July 2018

An maidawa Sheikh Gumi martani na cewa sha’anin tsaro ya cabe a Najeriya

Wani babban Malamin addini da ma Boko a Arewacin Najeriya Farfesa Salisu Shehu yayi wa fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan watau Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi raddi na cewa abubuwa sun tabarbare a Najeriya.


A wata hira da Babban Malami Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yayi da Jaridar Punch ya bayyana cewa sha’anin tsaro ya jagule sannan kuma harkar kiwon lafiya da sauran su duk sun cabe a lokacin Gwamnatin nan ta Shugaba Buhari.

Babban Malamin wanda yana cikin Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya tace akwai alamun karya a maganar da Malamin yayi na cewa sha’anin tsaro ya fi kyau a lokacin tsohon Shugaban kasa Jonathan yana mulkin kasar.

Farfesan yace a lokacin Jonathan sai da ta kai bangare da dama a Arewacin Kasar sun shiga hannun ‘Yan Boko Haram. Malamin yace Sheikh Gumi bai isa ya je irin su Maiduguri, Yola. Damaturu da sauran su yayi wannan magana ba.

Malamin na Jami’ar Bayero ta Kano ya nemi Malamin yayi wa Gwamnatin Buhari adalci kamar yadda addinin Musulunci ya koyar. Farfesa Shehu ya tunawa Gumi irin ta’adin da aka yi a Arewa ta wani dogon rubutu da yayi a a Facebook.
trthausa.

No comments:

Post a Comment