Sunday, 1 July 2018

An wulakanta Sheikh Sudais a kasar Switzerland

An wulakanta Sheikh Sudais a Geneva
An wulakanta limamin babban masallacin Makkah,Sheikh Sudais yayin da yake wa'azi a wani masallacin birnin Geneva na kasar Switzerland. Wasu 'yan Arewacin Afirka  2 sun far wa sheikh Abdul Rahaman Al Sudais, limamin masjidul Haram a wani masallacin birnin Geneva, yayin da yake wa'azi.


Matasan sun jefi Sudais da bakeken kalamai tare da tuhumar sa da daure wa shugabannin masarautar Saudiyya gindi a kashe-kashen bayin Allah da suke ci gaba da yi a Yaman, takunkuman da suka kakaba wa Qatar da kuma hawa kan kujerar naki game da batun shirya gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 a kasar Morocco,inji kafar yada labarai ta Al Khabar.
Matashi na farko dan kasar Algeria mai suna Saladdin Yakhlaf ya ce wa limamin,
"Kuna mana magana kan batun samar da zaman lafiya, amma kun yi wa 'yan uwanmnu na Qatar da Yaman kofar rago, kuna da hannu dumu-dumu a jinin  da aka zubar a shekarar 1992 da kuma juye-juyen mulki da aka yi a Masar da Turkiyya.Mun bar ka da Allah..Ka daure wa ahlin Sa'ud gindi...Ranar tashin kiyama sai Allah ya saka mana...Allah na kawo wa Bamaguje dauki indai adali ne, ya kuma juya wa Musulmi baya idan azzalumi ne...Ku ko kun kasance azzalumai".
Matashi na 2 dan kasar Morocco kuma cewa ya yi,
"Shin me yasa Saudiyya ke mara wa Amurkawa baya? Me yasa zuka jefa wa Amurka kuri'a yayin zaben tantance kasar da za ta karbi bakwancin wasannin cin kofin duniya na shekarar 2026, maimakon ku zabi Morocco".
A watanni baya ma, duniyar Islama ta yi caa kan Sudais sakamakon wani kalami da ya furta,inda ya ce a duk fadin duniya,Amurka da Saudiyya ne ke kai ruwa rana don tabbatar da zaman lafiya a ko ina.
trthausa.

No comments:

Post a Comment