Sunday, 8 July 2018

An yabawa shugabar kasar Croatia bisa zuwa kallon wasan kasar ta da tayi a Rasha

Shugabar kasar Croatia, Kolinda Grabar-Kitarovic taje kallon wasan da kasarta ta buga da kasar Rasha jiya a ci gaba da buga gasar cin kofin Duniya, zuwan nata gurin kallon wasan ya dauki hankulan mutane sosai.Tun daga jirgi inda ta shiga tare da sauran 'yan kasar, sannan kuma da halartar filin wasan an yaba mata da cewa hakan ya karawa 'yan kwallon karfin gwiwa.
Shugabar dai tana sanye da rigar 'yan kwallon kasar tata wadda ta dora wata jar riga a samata sannan sun zauna tare a guri na musamman da firaiministan Rasha, Dmitry Medvedev, bayan da aka ci Croatia kwallo kuma ta rama, Kolinda ta mikawa Medvedev hannu suka gaisa.

Haka kuma bayan da Croatia ta saka kwallo ta biyu shugabar ta tashi tayi zumbur daga kan kujerarta tayi murna yayin da shi kuma Medvedev ya kawar da kai cikin haushi. Ta kuma cire rigar data dora kan jasin da ta saka.

Wasan dai ya kare da bugun fenaret wanda Croatia tayi nasara akan Rasha.

Amma da dama sun yaba da kokarin ba zata da kasar Rasha ta nuna.

No comments:

Post a Comment