Friday, 13 July 2018

An zaɓi Obama a matsayin shugaban Amurka mafi adalci

Sakamakon hukumar binciken Pew ya nuna cewa Barack Obama ne shugaban da aka zaɓa mafi karamci a Amurka.


Haka kuma, sakamakon zaben jin ra'ayin jama'a na nuna cewa matar Barack Obama ka iya kasancewa mafi karamci daga cikin matan shugabannin kasashen Amurka da suka gabata.

Sakamakon zaben jin ra'ayin jama'a kaso 44 cikin ɗari ya bayyana Barack Obama a matsayin shugaban Amurka mafi adalci kasancewar wanda ya mulki ƙasar ta hanyar yiwa kowa aiki ba tare da nuna wariyar launin fata ba.

Sakamakon da hukumar zaɓen ta Pew Research Center ta fitar Bill Clinton ya zo na biyu da kuri'u kaso 33 cikin ɗari, sai kuma Ronald Reagan yazo na uku da kaso 32 cikin ɗari

An dai gudanar da zaben ne a tsakanin ranakun 5-12 ga watan Yuni inda mutane fiye da dubu biyu suka jefa kuri'a inda shugaba Donald Trump ya zo na ƙarshe.

Ana dai  kallon shugaba Trump a matsayin wanda ya fi raba kawunan jama'ar kasar Amurka
trthausa.

No comments:

Post a Comment