Monday, 9 July 2018

Ana shirin daure wani tsohon shugaban kasa tsawon shekaru 20 saboda cin dukiyar gwamnati

Mun ji cewa Shugaban kasar Malaysia mai shekara kusan 93 Mohathir Mohammed ya sa an damke tsohon Shugaban kasar bisa zargin wawure dukiyar al’umma da yayi lokacin yana kan karagar mulki a kasar ta Malaysia.

Labarin da ke mu samu daga kasar waje sun ce an yi ram da tsohon Shugaban kasar Malaysia Najib Rasak da ya sauka ne kwanan nan bisa zargin da ke kan san a tafka mugun satar da ba a taba ganin irin sa a kasar ba.

Hukumar yaki da barayin Gwamnati na kasar za ta maka Rasak a gaban Kotu inda za a tuhume sa da laifin cin amanar kasa da kuma wuce gona da iri a Gwamnati. Idan an same sa da laifi dai za a daure sa na shekaru 20.

The Guardian ta rahoto cewa wata badakalar IMDB ce ta ci tsohon Shugaban don haka Hukumar da ke binciken barayin Gwamnati na kasar MACC ta kama tsohon Shugaban a gidan sa da ke Garin Kuala Lumpur kwanaki.

Ana dai zargin Shugaba Najib da satar dukiyar jama’a wanda ta kai Dala Miliyan 681 lokacin yana mulki don haka sabon Shugaban kasar ya nemi Jami’an kula da shiga-da-fice da su hana iyalin sa barin kasar tun da ya karbi mulki.

No comments:

Post a Comment