Tuesday, 10 July 2018

APC ta zargi gwamnan jihar Ekiti da biyan masu motocin haya na jihar dan kada su dauki masoya Buhari

Jam'iyyar APC reshen Ekiti ta zargi Gwamnan jihar, Ayodele Fayose da biyan dukkanin direbobi masu jigilar fasinjoji da ke jihar kudin aikinsu na yini inda suka ajiye motocinsu a gidan gwamnatin jihar don ganin ba su yi jigilar 'ya'yan jam'iyyar APC da aka tsara za su tarbi Shugaba Muhammad Buhari ba wanda zai halarci gangami jam'iyyar na takarar kujerar  Gwamnan jihar, Ayo Fayemi a yau Talata.

rariya.

No comments:

Post a Comment