Tuesday, 10 July 2018

Ashe Neymar da Mbappe basa shiri?: Karanta yanda Neymar din ke kiran Mbappe da sunan banza a PSG

Tauraron dan kwallon kafar kasar Faransa, Kylian Mbappe dan shekaru 19 ya je kungiyar kwallon kafa ta PSG daga Monaco a matsayin Aro wanda akwai damar sayenshi, dan kwallon ya taka rawar gani sosai.


Yaci kwallye 21 yayin da ya bayar da taimako akaci 16 a wasa 46 daya bugawa kungiyar.

Saidai wani rahoto da EL Pais suka wallafa ya bayyana cewa Neymar da Mbappe basa shiri a PSG.

Rahoton yaci gaba da bayanin cewa, Neymar da Dani Alves sun rika kiran Mbappe da wani sunan banza 'Donatello' suna mai dariya, wai dan suna tunanin yana kama da 'yan Cartoon dinnan na Mutant Ninja Turtle.

Haka kuma 'yan wasan sun rika fadin cewa, Mbappen be tsayawa yayi yanka da kwallo gudu kawai ya iya.

Iyalan Mbappe sun kai kara gurin kungiyar ta PSG akan wannan maganar inda sukace abokan aikin dansu da suka fishi shekaru suna matsa mishi basa barinshi walwala.

Rahoton yace PSG tayi kokarin sasanta wannan matsala kuma a kokarinta na kawo karshen wannan matsalar sun bukaci 'yan wasan da su rika wa juna magana da hudda me kyau a gaban mutane, PSG tayi fatan cewa kasashen Faransa da Brazil su hadu a wasan daf dana karshe na gasar cin kofin Duniya dan 'yan wasan su wa juna magana a bainar Duniya kowa ya gani, amma sai gashi an fitar da Brazil din.

Rahoton dai yace PSG tana ji da Neymar sosai kuma tana mishi abubuwan kyautatawa dan kada ya bar kungiyar, haka kuma kungiyar tana ganin abu ne me matukar wuya ace Mbappe yaci kofin Duniya tare da kasarshi ta Faransa.

Idandai Mbappe yaci kofin Duniya ana tunanin darajarshi zata iya wuce ta Neymar, amma ba'a tunanin PSG din zata bashi irin kulawar da take baiwa Neymar koda hakan ta kasance.

No comments:

Post a Comment