Tuesday, 31 July 2018

Ba kada Ganduje ne a gabanmu ni da Kwankwaso ba>>Shekarau


Tsohon gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce ba kada gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne a gabansu shi da Sanata Rabiu Kwankwaso ba.Shekarau ya bayyan hakane a wata hira da yayi da BBChausa inda yace ba su hadu guri guda shi da Kwankwaso ba dan su kada wani dan siyasa ba kuma duk wani abu da y faru a tsakaninsu ya wuce babu maganar tuna baya.

A makon jiya ne tsofaffin gwamnonin na Kano biyu suka gana a karon farko cikin shekaru da dama, kwanaki kadan bayan Kwankwaso ya sauya sheka daga APC zuwa PDP inda ya tarar da Shekarau.

No comments:

Post a Comment