Thursday, 12 July 2018

BADAKALAR MINISTA KEMI: Gwamnatin Buhari ta yi magana kan satifiket din ta na NYSC

gwamnatin Najeriya ta yi magana a karon farko dangane da bahallatsar Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun wadda ta mallakai shaidar sahale mata aikin bautar kasa na NYSC, amma na bogi.


Wakilin PREMIUM TIMES a fadar Shugaban Kasa, ya ritsa Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, inda ya jefa masa wannan tambayar, kuma ya nemi amsa.

Minista Lai yace ai babu wani abu da zai iya kara cewa, domin Hukumar NYSC ta rigaya ta yi magana.

“Hukumar NYSC ai wani bangare ne na gwamnati, kuma ta yi magana. Don haka babu wani abin da zan iya karawa.” Inji Lai.

Wannan ne karon farko da wani jami’in gwamnatin Muhammadu Buhari ya furta wani abu dangane da harkallar Kemi.

Tabbatattu kuma sahihan shaidun bayanai rubutattu sun tabbatar da cewa Ministar Harkokin Kudi, Kemi Adeosun ba ta yi aikin bautar kasa ba, kuma a lokacin shekarun ta ba su kai na wadda aka dauke wa aikin bautar kasar ba.

No comments:

Post a Comment