Sunday, 1 July 2018

Bafarawa Ya Amince Zai Fito Takarar Shugaban Kasa

Ni Majidadin Bafarawa daga yau na janye karar da na yi ikirarin cewa zan kai Maigidan kotu idan bai tsaya takar shugabancin kasar nan ba.


Alhamdulilah a yau ne tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Dr Attahiru Dalhatu Bafarawa kuma abun alfarin mu ya amsa kiran 'yan Nijeriya masu cewa ya fito takarar shugabancin kasar nan.

 Muna kara godiya a gare shi da ya amsa kiran 'yan Nijeriya. Allah ubangiji muna rokonka, mun yi tawassali da sunayen ka tsarkaka Allah kamar yadda Maigidan mu ya amsa wannan kira namu ya Allah kaba shi shugabancin kasar nan.
rariya.

No comments:

Post a Comment