Friday, 13 July 2018

Bangaren su Shehu Sani ya fice daga APC


Bangarori biyu na jam'iyyar APC a jihar Kaduna wato Akida da kuma 'yan Restoration sun bayyana ficewarsu daga jam'iyyar a ranar Juma'a.Sun bayyana hakan ne a lokacin wani taro da bangarori biyu, wadanda suke samun goyon bayan 'yan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani da Suleiman Hukunyi, suka yi a birnin Kaduna.

Har ila yau 'yan siyasar wadanda ba sa jituwa da gwamnatin jihar, sun bayyana "yanke kauna da kuma dukkan wata alaka da jam'iyyar."

Sai dai ba su bayyana jam'iyyar da za su koma ba tukunna.

Amma Sanata Shehu Sani da Sanata Hunkuyi ba su halarci taron ba.

Wani jigo a bangaren da suka fice, Mataimaki Tom Mai Yashi, ya shida wa BBC cewa "mun dauki matsayar ne bayan mun tattauna da dukkan mambobinmu. Mun bar jam'iyyar APC har abada."

Sai dai bangaren uwar jam'iyyar a jihar ya mayar da martanin cewa 'yan siyasar sun yi hakan ne ba domin bukatun al'ummarsu ba, sai domin biyan bukatun kansu.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment