Sunday, 1 July 2018

Bani da burin siyasa Kwallo ce a gabana>>Ahmed Musa

Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya fito ya bayyana cewa shi bashi da ra'ayin neman wani mukamin siyasa, kwallo ce a gabanshi, bayan da Musa ya ciwa Najeriya kwallaye biyune a gasar cin kofin Duniya wasu 'yan Najeriya suka fara hada hotunanshi a matsayin shugaban kasa.


Shafin Daily Post ya ruwaito cewa, Ahmed Musa ya bayyana cewa yana taimakawa mutanen da basu da karfi dan canja rayuwarsu kuma zai ci gaba da hakan, sannan kuma bashi da burin tsayawa takarar siyasa, kwallo ce a gabanshi.

No comments:

Post a Comment