Friday, 13 July 2018

Bankin duniya ya ba wani matashi dan Arewa babban mukami

Babban bankin duniya ya nada wani matashi mai suna Muhammad Abdullahi dake zaman kwamishinan tsare-tsare da kuma kasafin kudin gwamnatin jihar Kaduna a matsayin mamba a majalisar ta mu'amala da mutane watau Expert Advisory Council on citizen engagement a turance.


Kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta DailyNigerian, Mista Muhammadu Abdullahi, kwararre ne a harkokin tattalin arziki kuma yanzu zai hadu ne da wasu mutane biyar daga sassa daban-daban na duniya domin yin aikin.

A cikin takardar nadin ta sa, babban bankin yayi ta kwararawa matashin yabo tare da zayyano kwarewar sa da ta sa ya samu nadin.

No comments:

Post a Comment