Friday, 13 July 2018

Buba Galadima Ya Nemi Kotu Ta Mika Masa Ragamar Shugabancin APC

Shugaban bijirarrun jam'iyyar APC na kasa, Buba Galadima ya shigar da kara Babban kotun tarayya inda yake neman a rusa zaben shugabannin APC na kasa da aka gudanar kwanaki.


Ya kuma nemi kotu ta mika masa ragamar jagorancin jam'iyyar a matsayin na riko kafin a sake yin wani sabon zaben. Wannan mataki na Buba Galadima ya biyo bayan wata wasika ce da ya aikawa hukumar zabe mai zaman kanta inda ciki ya nemi hukumar ta ki amincewa da sabbin zababbun shugabanni APC na kasa.
rariya.

No comments:

Post a Comment