Sunday, 8 July 2018

Buffon ya saka hannu dan bugawa PSG wasa na tsawon shekara daya

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta bayyana saka mata hannu da tauraron gola Gianluigi Buffon yayi na buga mata wasa har na tsawon shekara daya.A yarjejeniyar daya sakawa hannu dan shekara araba'in din zai iya kuma sake saka hannu dan ci gaba da bugawa PSG din bayan shekara daya idan yana so, kungiyar da bayyana hakanne a wani bidiyo da ta saka inda aka ga Buffon sanye da rigar kungiyar

Buffon ya bayyana cewa zai yi iya kokarinshi dan bayar da gudmummawa wajan cimma burin PSG.

No comments:

Post a Comment