Tuesday, 3 July 2018

Buhari: Dole a dawo wa da Afirka dukiyoyinta da aka sace

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya zama wajibi a dawo wa da Kasashen Afirka dukiyoyinsu da aka sace ba tare da aiki da wasu dokoki marasa amfani ba.


Buhari ya bayyana hakan a yayin taron da Tarayyar Afirka ta fara a Nuwakshot Babban Birnin Muritaniya mai taken "Hanya Mai Dorewa don Sauya fasalin Afirka: Yaki da Cin Hanci da Rashawa." inda ya ce, kasashen Afirka na bukatar shugabanci mai adalci da kuma bayar da goyon bayan kowanne bangare.

Shugaba Buhari ya ce, dole ne a dawo wa da Afirka arzikinta da aka sace ba tare da duba da dokokin kasashe da suke hana dawo da su ba. 

Ya ce, cin hanci da rashawa ya yi mumunan tasiri a kan al'uma kuma sun dauki watanni 6 suna aiyukan sanar da su hakan.

Buhari ya kuma yi kira da cewa, ya kamata dukkan Kasashen Afirka su sanya hannu kan yarjejeniyar Yaki da Cin hanci ta Tarayyar Afirka a wannan shekarar tare da fara aiki da ita wadda za ta bayar da damar musayar bayanai, taimakon shari'a da doka tare da kyawawan hanyoyin yaki da cin hanci da rashawa da kasashen nahiyar suke amfani da su.

Jagoran Taron Shugaban Tarayyar Afika kuma Shugaban Kasar Ruwanda Paul Kagame ya ce, yaki da cin hanci na da hatsari sosai, amma barin yakin ya fi zama hatsari.

Kagame ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a saboda haka taron na da muhimmanci da ma'ana sosai. 

Shugaban Kasar Gana Nana Akupo-Addo kuma cewa ya yi kowa daya ne a gaban doka, kafin kowa ya zama shugaban kasa, minista, dan majalisa ko dan sanda sai da ya fara zama dan kasa tukunna.

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Kudu Matemala Cyril Ramaphosa kuma cewa ya yi, idan ba a dauki mataki ba, to cin hanci zai hana rayuwar al'uma inganta.
Trthausa.

No comments:

Post a Comment