Friday, 13 July 2018

Buhari ya nada Dauda Rarara a matsayin daraktan wakoki na kasa

Fadar shugaban kasa, ta ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya ta nada shahararren mawakin nan na Kano, Dauda Rarara a matsayin daraktan waka na kasa kan kwamitin magoya bayan Buhari a 2019.


Babban mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin lamuran siyasa, Gideon Sammani, wanda ya bayyana akan a wata sanarwa yace kwamitin zai samu jagorancin tsohon shugaban PDP na kasa, Ali Modu Sharif a matsayin darakta janar.

Sauran wadanda aka nada a kwamitin sun hada dad an wasan Nollywood kuma dan majalisar jihar Lagas Hon Desmond Elliot a matsayin babban sakataren labaran kwamitin na kasa, da kuma shugaban ma’aikata na gwamnan jihar Imo kuma dan takarar gwamna a APC, Uche Ugwumba Nwosu a matsayin babban sakatare.No comments:

Post a Comment